Rundunar ‘yansandan jihar Rivers ta ce ba za ta bari a yi zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka tsara gudanarwa gobe Asabar ba.
wata sanarwa da kakakin ‘yansandan jihar, SP Grace Iringe-Koko ya fitar, ya ce rundunar ta samu umarnin kotu da ya hana su bayar da tsaro a lokacin zaɓukan.
Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar 30 ga watan Satumba babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramta wa rundunar barin gudanar da zaɓen da kuma bayar da tsaro a lokacin zaɓen.
‘Kan haka ne sashen shari’a na rundunar ‘yansandan ya shawarci rundunar cewa ta yi biyayya ga umarnin kotun”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Shi dai gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya dage cewa sai an gudanar da zaɓen duk da wannan umarni na kotu.