Ƴan siyasa ne ke haifar da ƙaruwar shaye-shaye ga matasa – Kawu Sumaila
Kawu Sumaila, Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, ya ce wasu ‘yan siyasa da bai fadi sunayensu ba na haddasa yawaitar amfani da miyagun kwayoyi a kasar nan.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Sumaila ya yi wannan jawabi ne a yau Talata a zauren majalisar dattawa, yayin da ya ke ba da gudunmuwa a muhawara kan kudirin dokar da ke neman kafa cibiyar kasa ta wayar da kan jama’a game da amfani da kwayoyi da kuma gyaran hali.
Sanata Rufai Hanga wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya, shi ne ya gabatar da kudirin.
Sanatan mai wakiltar Kano ta kudu ya bayyana cewa wasu daga cikin gidajen ‘yan majalisa da ofisoshin mazabu ana amfani da su wajen boye kwayoyi ta hannun ma’aikatansu.
Shugaban kwamitin wasanni ya ce ya zama dole a rika tilasta wa ‘yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati yin gwajin kwayoyi kafin a gudanar da zabe ko nada su mukami.
“Dole mu samar da yanayin da kafin a gudanar da zabe ko nada mukami, sai an yi gwajin kwayoyi,” in ji shi.
“Yayin da nake magana yanzu, yawancin jami’anmu a mazabunmu, yawancin jami’an siyasa, yawancin gidajenmu, idan ka shiga, za ka ga tarin kwayoyi a can.”