Amurka ta yi barazanar katse tallafin makamai ga Isra’ila kan Gaza
Amurka ta rubuta wa gwamnatin Isra’ila wasiƙa inda ta ba ta kwana 30 da ta ƙara yawan kayan agajin da ake kai wa Gaza ko kuma ta katse tallafin makaman da take ba ta.
Wasiƙar dai ita ce wani saƙo mafi zafi da gwamnatin Biden ta taɓa aikewa zuwa babbar ƙawarta wato Amurka tun bayan fara yaƙi a Gaza shekara guda.
Takardar wadda aka aike da ita kwana biyu ta samu sa-hannun sakatare ƙasashen wajen ƙasar,
Anthony Blinken da sakataren harkokin tsaro, Lloyd Austin, ta ce Amurka na cikin damuwa kan taɓarɓarewar yanayin jinƙai a Gaza.
Har wa yau, wasiƙar ta ƙara da cewa Isra’ila a watan da ya gabata ta ƙi amince wa ko kuma ta daƙile kaso 90 na harkokin jinƙai arewacin Gaza.
Wasiƙar ta kuma ambaci umarnin da Isra’ilar ke bai wa jama’a na su bar yanki inda ta ce umarnin ya tilasta mutane fiye da miliyan 1.7 yin tururuwa zuwa bakin ruwa inda rayuwarsu ke fuskantar barazana kamuwa da cutukan da ka iya sa su rasa rai.
Daga ƙarshe wasiƙar ta bai wa Isra’ilar wa’adin wata guda na “ɗaukar matakan gaggawa wajen magance matsalar”.
“Dole ne Isra’ila ta ta fara aiki daga yanzu zuwa kwana 30 wajen ɗaukar ƙwararan matakai domin bai wa kayan agaji damar shiga”, inda ta ƙara da cewa gaza yin hakan “na da tasiri kan tsare-tsaren Amurka.”