Daga Abdulaziz Abdulaziz
A ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2024, Jaridar Daily Trust ta fito ta nemi gafarar al’umma da gwamnatin tarayya bisa labarin da ta wallafa a ranar 4 ga watan Yuli, 2024 kan yarjejeniyar (Sàmòa) wanda ba gaskiya ba ne.
yabo be ga hukumar gudanarwar kamfanin na Media Trust. Ba kowa ne ke da sauƙin kan karɓan wani kuskure da yayi ba. Yanzu dai komai ya daidaita ta.
Labarin da suka buga a ranar 4 ga watan Yuli, 2024 wanda ya tada ƙura shi ne zargin cewa yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya da sauran ƙasashen Karebiyan da Fasifi suka sanyawa hannu
da ƙungiyar tarayyar Turai (EU) ta ƙunshi kare haƙƙin masu neman jiñși. Wanda hakan zai ba su damar cin gajiyar Dala Biliyan 150. Abin mamaki babu wata hujja da suka bayyana wacce ke tabbatar da zargin.
A jawabin neman afuwar da ta fitar, Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ta gamsu da binciken da kwamitin ɗa’ar aikin jarida ya gabatar. Rahoton
kwamitin wanda aka fitar a ranar 23 ga watan Satumba, 2024 biyo bayan ƙorafi da gwamnatin tarayya ta shigar, ya gano cewa duk cikin shafuka 403 na
yarjejeniyar Samoa babu inda aka yi maganar ƙasashe masu tasowa ko manyan ƙasashe na Duniya za su goyi baya ko kare haƙƙin masu neman jinsi a matsayin sharaɗin samun tallafi ko wani taimako daga manyan ƙasashen Duniya.
Kuma babu ma inda aka yi maganar masu neman jinsi kwata-kwata a cikin yarjejeniyar.
Tun da farko na kaɗu da jin labarin a matsayina na ƙwararre kafin komai. Na yi rubutu a Social Media kan yadda aka samu raunin cika ƙa’idojin aikin jarida kamar kafa hujja.
Wannan shi ne tsokacin da zan yi ko da ba na cikin gwamnati. Magana ta gaskiya har yanzu ina mamaki ta yaya labarin ya kai ɗakin buga labarai na Jaridar gaskiya, inda na yi aiki na san yadda aikin tace labari yake.
Labarin ya sanya damuwa a zukatan mutane. Saboda labarin ya zo ne daga kafar gaskiya wanda kowa yana tunanin in dai labari ya fito daga gare ta gaskiya ne. Labarin ya fita ranar Alhamis,
hakan ya sanya mutane da dama a Arewa musamman Malamai suka yi maganganu a kai. Banga laifinsu ba saboda labarin ya zo ne daga kafar gaskiya.
Bayan mutane sun fusata, wasu kuma daga ƴan adawa sun ƙara ruru wutar.
Sun yi amfani da wasu malaman addinin domin su ƙalubalanci gwamnati.
Washegarin ranar da abin ya faru haka limamai suka hau mimbari a fusace da labarin da ba shi da tushe.
Shugaba Tinubu da gwamnatinsa da duk ɗinmu da muke aiki da ita ba tayadda za mu sayar da Najeriya domin ɗaga darajar masu neman jinsi.
Kuma ma Najeriya tana da dokokin da suka haramta neman jinsi, babu yadda za a yi a shigo da abin da ya ci karo da dokar ƙasa.
Aikin jarida aiki ne da ke buƙatar lura da takattsan da tafikarwa bisa hujja.
Sardauna da yake ƙaddamar da tawagar jaridar Najeriya yayi musu gargaɗi da cewa “ku faɗi gaskiya a kan mu, kuma ku faɗa mana gaskiya akan wasu”.
Ba abin da muke buƙata bayan haka.
Abdulaziz, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan sadarwa.