News

El-Zakzaky: Kotu ta umarci ‘yan sandan Najeriya su biya ‘yan shi’a N15m

Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta umarci ‘yan sandan Najeriya su biya ‘yan kungiyar Shi’a mabiya Shaikh Ibrahim Elzakzaky Naira miliyan 15 saboda kisan ‘ya’yan kungiyar uku yayin wata zanga-zanga a Abuja.

Kotun wacce ta yi zamanta a Abuja babban birin kasar ta kuma umarci babban asibitin kasa ya bayar da gawarwakin uku nan take domin yi musu jana’iza.

A ranar 22 ga watan Yulin 2019 ne aka kashe wasu mabiya kungiyar ta Shi’a yayin wata zanga-zanga da ta rikide zuwa tarzoma.

A lokacin zanga-zangar su ma ‘yan sanda sun yi zargin cewa ‘yan Shi’a sun kashe dan sanda, zargin da kungiyar ta IMN ta musanta.

Lauyan kungiyar ta IMN Bala Isa Daku ya ce sun garzaya kotun ne bayan hukumomi sun ki ba da gawawwakin domin yi musu jana’iza.

A hukuncin kotun karkashin mai shari’a Taiwo Taiwo, ya ce ‘yan sanda za su biya Naira miliyan ga kowane mamaci a matsayin diyyar kisan da aka yi.

Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar cewa a tilasta wa ‘yan sanda su nemi afuwar kisan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Latest News

To Top